Mar 02, 2019 09:40 UTC
  • An Fallasa Kokarin Hadaddiyar Daular Larabawa Na Gurgunta Demokradiyar Tunisiya

Tsohon Firai Ministan kasar Tunisia ya bayyana cewa gwamnatin kasar Hadaddiyar daular larabawa tana da hannu a kokarin gurgunta demokradiyar kasar Tunisiya.

Kamfanin dillancin labaran Fars na kasar Iran ya nakalto Hammadi Aljabali tsohon firai ministan kasar Tunisiya yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa gwamnatin Emerate tana son ganin bayan jam'iyyar Annahdah a kasar, sannan tana taimakawa wasu kungiyoyin yan ta'adda don kashe Shukri Bal-id daya daga cikin shuwagabannin yan adawar kasar a shekara ta 2013.

Aljabali ya kara da cewa gwamnatin Emaret tana kashe kudade masu yawa don lalata tsarin democradiyya da kuma gurgurta gwamnatocin wasu kasashen larabawa wadanda suka hada da Siriya, Yemen da Libya. 

Har'ila yau Munsif Almarzuki tsohon shugaban kasar ta Tunisiya shi ma, ya sha nanata cewa gwamnatin Emaret ko hadaddiyar daular larabawa tana son gurgunta tsarin demokradiyyar kasar Tunisia don bata son tsarin domokradiyya a kasashen.

Tags