Pars Today
Tsohon Firai Ministan kasar Tunisia ya bayyana cewa gwamnatin kasar Hadaddiyar daular larabawa tana da hannu a kokarin gurgunta demokradiyar kasar Tunisiya.
Paparoma Francis shugaban cocin batholica na duniya wanda ya ke ziyara a kasashen Latabawa ya tabbatar da cewa akwai matsalar muggan halaye na wasu malaman cocinsa dangane da lalata da yara da kuma mata.
Paparoma Francis shugaban Cocin Catholica ya isa birnin Abudabi na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ko UAE a yau Litinin inda ya gana da yerime mai jiran gado na kasar Mohammad bin Zayed Al-Nahyan.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa ficewar Amurka daga yerjejeniyar Nukliyar Iran ta shekara ta 2015 ya maida Amurka saniyar ware a duniya.
A dazu-dazun nan ne majalisar dattawan kasar Amurka ta amince da kuduri biyu wadanda suka bukaci gwamnatin kasar ta dakatar da tallafin da take bawa gwamnatin kasar Saudiya da kawayenta a yakin da suke yi a kasar Yemen.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Yemen ta kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su dorawa Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa laifin kallafawa mutane Yemen yaki da kuma laifukan da ke tattare da shi.
Wasu majiyoyi a kasar Libya sun bayar da bayanai dangane da wata ganawa tsakanin Saiful Islam Ghaddafi dan tsohon shugaban Libya marigayi Kanar Ghaddafi, da kuma wasu jami'an gwamnatocin masar da kuma hadaddiyar daular larabawa.
Rahotani sun ce hadaddiyar daular larabawa tana taimakawa 'yan ta'addar Libiya da makamai.
Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ta sanar da cewa: Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ce ke da alhakin aiwatar da munanan matakan cin zarafin bil-Adama a kasar Yamen.
Sheikh Muhammad Bin Rashid Al Maktum sarkin Dubai ya caccaki mahukuntan kasashen larabawa kan abin da ya kira rashin iya tafiyar da mulki a kasashensu.