Dec 14, 2018 11:47 UTC
  • Pentagon: Amurka Na Bin Saudia Da Kawayenta Bashin Dalar Biliyon 331.

A dazu-dazun nan ne majalisar dattawan kasar Amurka ta amince da kuduri biyu wadanda suka bukaci gwamnatin kasar ta dakatar da tallafin da take bawa gwamnatin kasar Saudiya da kawayenta a yakin da suke yi a kasar Yemen.

Shafin yanar gizo na ma'aikatar tsaron kasar Amurka, ko Pentagon ya nakalto kakakin ma'aikatar yana cewa gwamnatin Amurka tata tattauna da Saudia da kawayenta don biyanta bashin dalar Amurka biliyon 331 saboda makamashin da ta yi ta bawa jiragen yakin Saudia da kawayenta a yakin da suke yi a kasar Yemen.

Labarin ya kara da cewa Pantagon, ta bayyana wannan labarin ne jin kadan bayan da majalisar dattawan Amurka ta kada kuri'ar amincewa da kudurori biyu da kan kasar Saudia. Pentagon ta ce ta gano cewa kudaden da ta karba daga kawancen saudiya bai kai yadda yakamata ta karaba ba. 

 A jiya Alhamis ne yan majalisar dattawa 56 suka amince a yayin da 41 suka ki amincewa da kudurin biyu, wadanda suka bukaci Amurka ta dakatar da tallafawa wadannan kasashen larabawa, sannan ta dauki Mohammad bin Salman a matsayin wannan ya halaka Jamal Khashaggi.

Tags