Kotun ICC, Ta Yi Watsi Da Sallamar Laurent Gbagbo
(last modified Thu, 17 Jan 2019 04:06:20 GMT )
Jan 17, 2019 04:06 UTC
  • Kotun ICC, Ta Yi Watsi Da Sallamar Laurent Gbagbo

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC, ta dakatar da sakin tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, bayan da masu shigar da kara na kotun suka daukaka kara.

Da jiya Laraba ne, alkalan kotun suka bukaci a sallami tsohon shugaban kasar da kuma tsohon ministansa Charles Blé Goudé, bayan wanke su daga tuhume tuhumen da ake masu na cin zarafin bil adama.

Saidai kotun ta ICC, ta ce mutanen biyu, zasu ci gaba da kasancewa karkashinta har zuwa lokacin da aka saurari karar aka daukaka kansu.

A ranar Talata, data gabata ne alkalan kotun, suka zartar da hukuncin na sakin Mr Gbagbo, da Ble Goude bisa cewar basu da wani laifi, duba da yadda masu shigar da kara suka gaza bayar da gamsasshiyar shaida kan tuhume-tuhumen da ake masu, a don haka alkalan suka bada umarnin a sake shi ba tare da wata-wata ba.

M. Laurent Gbagbo, wanda shi ne wani tsohon shugaban kasa na farko da aka gurfanar a gaban kotun ta ICC, ana zarginsa da laifukan cin zarafin bin adama a tarzomar data biyo bayan zaben kasar a tsakanin 2010 zuwa 2011, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu uku a cikin watanni biyar.

Tsohon shugaban kasar ta Ivory Coast, ya kwashe shekaru bakai a hannun kotun ta ICC dake birnin Hague.