An Bukaci Gwamnatin Sudan Ta Janye Sojojinta Daga Kasar Yemen.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30450-an_bukaci_gwamnatin_sudan_ta_janye_sojojinta_daga_kasar_yemen.
'Yan Majalisar Kasar Sudan sun bukaci janye sojojin kasar cikin gaggawa daga kasar Yemen.
(last modified 2018-08-22T07:01:46+00:00 )
Apr 30, 2018 14:42 UTC
  • An Bukaci Gwamnatin  Sudan Ta Janye Sojojinta  Daga Kasar Yemen.

'Yan Majalisar Kasar Sudan sun bukaci janye sojojin kasar cikin gaggawa daga kasar Yemen.

Tashar talabijin din Aljazeera ta nakalto majiyoyin kasar Sudan na cewa wakilan 'yan majalisar dokokin kasar sun gana da shugaba Umar Al-Bashir inda suka bukaci shi da ya dauki matsaya ta siyasar ba ruwa na wajen magance rikici da kuma tabbatar da sulhu a kasar Yemen.

Har ila yau 'yan majalisar ta Sudan sun bukaci gwamnati da ta dauki nauyin iyalan jami'an tsaron da suka rasa rayukansu a kasar ta Yemen.

A cewar wakilan 'yan majalisar dokokin kasar ta Sudan, adadin jami'an tsaron kasar da suka hallaka ko kuma jikkata a kasar ta Yemen sun haura zuwa dari.

Tun a watan Maris din 2015 ne kasar Sudan ta shiga cikin kawancen wasu kasashen Larabawa bisa jagorancin Saudiya wajen kadamar da hare-haren  wuce gona da iri kan al'umma kasar Yemen, inda ta tura sojoji kimanin dubu hudu.