Pars Today
Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayya Afrika, sun bukaci ganin an warware rikicin kasar Libiya, ta hanyar siyasa.
Shugagba Félix Tshisekedi, na Jamhuriya Demokuradiyyar Congo ya yi afuwa wa fursunonin siyasa 700 na kasar.
Kafar watsa labaran Arabie News ta nakalto Mohamed Tahir Ayala Piraministan kasar Sudan a wannan Laraba yayin da yake mayar da martani kan ci gaba da kin jinin gwamnatin Omar al-Bashir na cewa nan ba da jimawa ba za a kafa sabuwar gwamnati a kasar.
Rundunar tsaron kasar Mali ta sanar da mutuwar sojojinta shiga sanadiyar tashin Nakiya a tsakiyar kasar
Firaministar Birtaniya Theresa May ta sake shan kaye a gaban Majalisar kasar, inda ‘yan Majalisu 391 suka yi watsi da yarjejeniyar da May ta kulla da kungiyar Tarayyar Turai kan ficewar kasar daga cikinta.
Rahotanni daga jihar Lagas a Najeriya na cewa akalla kananan yara 10 ake fargabar sun makale a baraguzan gine-gine bayan rugujewar wani gini mai hawa 3 a unguwar Itafaji da ke jihar.
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa kisan daruruwan fararen hula a rikicin kabilancin dake faruwa a kasar Demokaradiyar Congo na a matsayin cin zarafin bil-adama.
Kungiyoyi da jam'iyyun adawa a kasar Sudan za su gudanar da wani zama a birnin Paris na kasar Faransa, domin tattauna hanyoyin kawo karshen matsalolin da kasar ta samu kanta a ciki.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel macron ya jinjina wa shugaban kasar Aljeriya Abdulaziz Butaflika kan janyewa daga takarar shugabancin kasar da ya yi.
Majalisar dinkin duniya ta kirayi gwamnatin Afghanistan da kuma kungiyar Taliban da su shiga tattaunawa.