Pars Today
Hyukumar lafiya ta duniya ta bayar da rahoton bullar wata cutar kwalera mai kisa a kan iyakokin kasashen Uganda da kuma Congo.
An rage yawan wa'adin aiwatar da dokar ta- baci a fadin kasar Sudan daga shekara daya zuwa watanni 6.
Shugaban kasar Aljeriya ya janye daga takarar neman shugabancin kasar a wani wa'adi na biyar.
Rundunar sojin kasar Masar ta sanar da halaka 'yan ta'adda 46 a cikin yankin Sinai ta arewa.
Fiye da alakalai 1000 ne a kasar Aljeriya suka bi sahun masu adawa da tsayawa takarar shugaban kasar a karo na biyar.
A Najeriya a yayin da ake ci gaba da fiatar da sakamakon zaben gwamnonin jihohin kasar, rahotanni daga kasar na cewa Jam’iyyar PDP ce ke kan gaba a jihohin Kano da kuma Bauchi.
Majalisar dokokin kasar Habasha ta ayyana zaman makoki na kwana guda yau Litini, domin juyayin mutane 157 da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin saman fasinja na kamfanin Ethiopian Airlines.
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya yi wa wasu daga cikin manyan jami'an sojin kasar ritaya.
kakain majalisar wakilai a Najeriya Yakubu Dogara ya yi tir da Allawadai da kisan wani dan majalisar wakilai ta tarayya da aka yi a cikin jahar Oyo.
A yau ne wani jirgin saman fasinja na kamfanin Ethiopian Airlines, kirar Boeing 737 ya fadi dauke da fasinjoji 149, da ma'aikatansa 8.