Aljeriya: Fiye da Alkalai 1000 Sun Bukaci Butaflika Ya janye Takararsa
Fiye da alakalai 1000 ne a kasar Aljeriya suka bi sahun masu adawa da tsayawa takarar shugaban kasar a karo na biyar.
Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a yau alkalai fiye da dubu daya sun fitar da bayani na hadin gwiwa, inda suka bayyana cewa, idan har Butaflika ya tsaya takarar shugabancin kasara zabe mai zuwa, to kuwa za su haramta sakamakon zaben.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dukkanin alkalai na kotunan Bujaya suka sanar da cewa sun bi sahun masu zanga-zangar nuna adawa da tsayawa takarar shugabab Butaflika.
A daya bangaren kuma lauyoyi fiye da dari biyar ne suka bude wani zaman dirshan a gaban babban kotun birnin Algiers fadar mulkin kasar ta Aljeriya, domin nuna rashin amincewarsu da takarar Butaflika.
Wannan na zuwa ne dai a lokacin da ministan shari’a na kasar ya kirayi dukkanin lakalan kasar da sauran bangarorin shari’a da kada su saka kansu a cikin batutuwa da suka danganci siyasa.