An Rage Yawan Lokacin Dokar Ta-Baci A Kasar Sudan
Mar 12, 2019 05:45 UTC
An rage yawan wa'adin aiwatar da dokar ta- baci a fadin kasar Sudan daga shekara daya zuwa watanni 6.
Tashar talabijin ta Sky News ta bayar da rahoton cewa, majalisar dokokin kasar Sudan ta rage yawan wa'adin gudanar dokar ta-baci a kasar zuwa watanni 6, bayan da shugaban kasar ya shelanta dokar har tsawon shekara guda a kwanakin baya.
Tun kafin wannan lokacin dai wasu daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar ta Sudan sun gabatar da wani daftarin kudiri da ke yin kira da a rage tsawon lokacin aiwatar da dokar, saboda a cewarsu hakan zai cutar da jama'a.
An kwashe kusan watanni uku ana gudanar da zanga-zanga a kasar ta Sudan, wadda ta fara tun daga ranar 19 ga watan Disamban 2018, domin nuna rashin amincewa da tashin fashin burodi da kuma makamashi, daga bisani kuma ta rikide ta koma ta kyamar gwamnatin Albashir.
Tags