Dogara Ya Yi Allawadai Da Kisan Wani Dan Majalisar Tarayya A Oyo
kakain majalisar wakilai a Najeriya Yakubu Dogara ya yi tir da Allawadai da kisan wani dan majalisar wakilai ta tarayya da aka yi a cikin jahar Oyo.
Jaridar Punch da ake bugawa a Najeriya ta bayar da rahoton cewa, kakain majalisar wakilan Yalubu Dogara ya bayyana wannan aiki da cewa aiki ne na dabbanci.
Jami'an tsaro a jahar Oyo sun tabbatar da cewa wasu mutanen ne da ba a san ko su wane ne ba suka harbe dan majalisare mai suna Olatoye Temitope Suga a wurin zabe a jiya Asabar a cikin garin Ibadan bababn birnin Jihar Oyo.
Dan majalisar dai ya je majalisar ne karkashin inuwar jam'iyyar ADP, duk kuwa da cewa bai samu nasarar komawa kan kujerarsa ba a zaben 'yan majalisar tarayya da aka gudanar.
Babu wani mutum ko gungun wasu mutane da suka dauki nauyin kisan dan majalisar, hakan nan kuma babu wasu bayanai daga bangaren jami'an tsaro kan ko ana tsare da wasu da ake zargi da hannu cikin lamarin.