WHO: An samu Bullar Kwalera A kan Iyakokin Uganda Da Congo
(last modified Tue, 12 Mar 2019 14:55:35 GMT )
Mar 12, 2019 14:55 UTC
  • WHO: An samu Bullar Kwalera A kan Iyakokin Uganda Da Congo

Hyukumar lafiya ta duniya ta bayar da rahoton bullar wata cutar kwalera mai kisa a kan iyakokin kasashen Uganda da kuma Congo.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a cikin rahoton na hukumar WHO, wasu daga cikin mutanen da suka kamu da cutar sun rasa rayukansu.

Hukumar ta ce ma'aikatan kiwon lafiya na kasar Uganda sun yi saurin fahimtar bullar cutar da kuma daukar matakan gaggawa wajen tunkararta.

Rahoton na hukumar lafiya ta duniya ya ce, an samu wadanda suka kamu da cutar a cikin yankin Zumbo da ke kan iyakar Uganda da jamhuriyar dimukradiyyar Congo, kuma cutar tana kashe dan adam matukar dai ba a hanzarta daukar matakan ceto rayuwarsa ba a cibiyoyin kiwon lafiya.

Yanzu haka dai an kafa kwamitoci tsakanin Uganda da Congo da kuma hukumar lafiya ta duniya da za su gudanar da ayyukan hadin gwiwa tare da hukumar lafiya ta duniya.