Ethiopian Airlines : Ana Zaman Makoki A Habasha
Majalisar dokokin kasar Habasha ta ayyana zaman makoki na kwana guda yau Litini, domin juyayin mutane 157 da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin saman fasinja na kamfanin Ethiopian Airlines.
A cikin sanarwar da ya wallafa a shfinsa na twitterfira ministan kasar ta Habasha, Abiy Ahmed, ya ce an ayyana zaman makokin ne domin juyayin dukkan 'yan kasashen da suka mutu a hatsarin jirgin.
Akwai 'yan kasashen duniya mabambanta 35 dake jirgin, da suka hada da 'yan Kenya 32, 'yan Canada 18 sai kuma 'yan Habasha 8.
Da sanyin safiyar jiya Lahadi ne jirgin saman fasinja na kamfanin Ethiopian Airlines, kirar Boeing 737 ya fadi dauke da fasinjoji 149, da kuma ma'aikatansa 8.
Jirgin ya fadi ne muntina shida bayan tashinsa daga birnin Adis Ababa na kasar Habasha zuwa Nairobin kasar Kenya.