Macron Ya Jinjina Wa Butaflika Kan Janyewarsa Daga Takara
Shugaban kasar Faransa Emmanuel macron ya jinjina wa shugaban kasar Aljeriya Abdulaziz Butaflika kan janyewa daga takarar shugabancin kasar da ya yi.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Jibouti Isma'ila Umar Guelleh a yau a ziyarar da ya kai kasar, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce matakin da shugaba Butaflika ya dauka abin jinjinawa ne.
Macron ya ce hakika matakin da Butaflika ya dauka shi ne daidai, kuma yana fatan za a ci gaba da bin matakan da suka dace domin samun sauyin gwamnati a nan gaba ta hanyar lumana. Kamar yadda ya yabawa al'ummar Aljeriya kan yadda suka nuna hankali da sanin ya kamata wajen gudanar da jerin gwano domin nuna mahangarsu.
Shugaban kasar ta faransa yana gudanar da wata ziyarar aiki ne a gabashin nahiyar Afrika, inda ziyarar tasa za ta hada da kasashe daban-daba, bayan Jibouti kuma zai ziyarci wasu kasashen yankin.