Pars Today
A Najeriya, yau ne al'ummar kasar ke kada kuri'a a zaben 'yan zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi.
A Sudan jama'ar kasar da dama ne suka fito yau Alhamis domin gudanar da wata zanga zanga ta kalubalantarkafa dokar ta bacin da shugaban kasar Omar Al' Bashir ya kafa.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta kame mutane fiye da 300 bisa zarginsu da aikata ba daidai ba a lokacin gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dattijai da wakilai a wancan makon da ya gabata.
'Yan jarida akasar Masar sun yi kakakusar suka kan yadda gwamnatin kasar ta mika kai ga neman kyautata hulda da Isra'ila.
Gwamnatin Nijar, ta sanar da dage haramcin kamun kifi, da noman tattasai da kuma kasuwancinsa a jihar Diffa.
A Yau ne kasar Ghana take bikin cika shrekaru 62 da samun ‘yancin kai daga mulkin mallakar Birtaniya
Majalisar tsarin mulki a Senegal, ta yi na'am da sakamakon zaben shugaban kasar na ranar 24 ga watan Jiya, wanda shugaba Macky Sall, ya lashe a wani wa'adin mulki na biyu.
Yan takarar shugaban kasa guda 12 a zaben ranar 23 ga watan Febrerun da ya gabata a tarayyar Najeriya, sun taya shugaban Muhammadu Buhari farincin nasarar da ya samu a zaben na ranar Asabar.
‘Yansanda a kasar Kenya sun kira ministan kudin kasar Mr Henry Rotich a karo na biyu don amsa tambayoyi dangane da badakkalar gina madatsun ruwa guda biyu wadanda za’a kashewa miliyoyin dalar Amurka a kasar.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Uganda ta fitar da sanarwa wadda ta yi Magana akan alakarta da kasar Rwanda.