Kasar Uganda Ta Yi Watsi Da Zargin Da Rwanda Take Yi Mata
(last modified Wed, 06 Mar 2019 05:53:36 GMT )
Mar 06, 2019 05:53 UTC
  • Kasar Uganda Ta Yi Watsi Da Zargin Da Rwanda Take Yi Mata

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Uganda ta fitar da sanarwa wadda ta yi Magana akan alakarta da kasar Rwanda.

Sanarwar wadda ta zo a matsayin martani ga Zarge-zargen da kasar Rwanda  take yi ma Uganda , hakan ya haddasa dagulewar alaka a tsakaninsu.

Wani sashe na sanarwar ya yi watsi da zargin cewa kasar Uganda ta bayar  da mafaka ga ‘yan adawar kasar Rwanda kuma suna gudanar da ayyukan da suke cutar da kasar.

Har ila yau sanarwar ta ce; Babu yadda kasar Uganda za ta bari wasu mutane su zauna a cikinta domin cutar da kasar da take makwabtaka da ita.

Bugu da kari, Ugandan ta karyata cewa ta kame ‘yan kasar Uganda kuma tana azabtar da su.

Sai dai sanarwar ta bayyana takaicinta akan yadda kasar Rwanda take kawo tarnakin zirga-zirgar mutane da kuma haja, a tsakanin kasashen biyu.

Tun a makon jiya ne dai alaka a tsakanin kasashen biyu ta yi kamari, bayan da kasar Rwanda ta zargi Uganda da bai wa ‘yan adawa mafaka, sannan kuma ta rufe kan iyakokin kasashen biyu.