Mar 07, 2019 14:59 UTC
  • An Yi Zanga zangar Kalubalantar Dokar Ta Baci A Sudan

A Sudan jama'ar kasar da dama ne suka fito yau Alhamis domin gudanar da wata zanga zanga ta kalubalantarkafa dokar ta bacin da shugaban kasar Omar Al' Bashir ya kafa.

Dokar da aka kafa a ranar 22 ga watan Fabrairu da ya gabata ta tsawan shekara guda, ana dai mata kallon wani salo mahukuntan kasar na murkushe zanga zangar tsadar rayuwa data rikide zuwa ta kyammar shugaba Al'Bashir da aka jima anayi a wannan kasa.

Mafi yawan wadanda suka shiga zanga zangar ta yau a Khartoum babban birnin kasar da wasu biranen kasar mata ne, dake furta kallaman nuna kiyaya ga shugaban kasar.

Tun a ranar 19 ga watan Disamba na shekara data gabata ne al'ummar kasar suka fara zanga zanga biyo bayan matakin gwamnatin kasar na kara farashin bredi, a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tattalin arziki.

Tags