Pars Today
Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhuni ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan Aya. Hashimi Shahrudiya shugaban majalisar maslahar tsarin mulkinn JMI kum tsohon alkalin alkalan kasar wanda Allah yayiwa rasuwa a jiya da yamma.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Jawad Zarif ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata jira kasashen turai su cika alkawarin da suka dauka dangane da yerjejeniyar nukliyar kasar ba.
Karamin ministan kiwon lafiya da kuma ilmin kiwan lafiya ya bayyana cewa JMI ta iran ce kasa ta farko a fagen ci gaban ilmi a yankin gabas ta tsakiya.
Kwanaki kadan bayan da Shugaba Donald Trump na AMurka ya bayyana shirin janye sojojin kasarsa daga Siriya, Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta bayyana hakan da cewa, tun farko dama kasancewar sojojin na Amurka a Siriyar kuskure ne.
Shugaban hukumar leken asiri na kasar Amurka ya sake nanata zargin kokarin yin tasiri na kasashen Rasha, Cana da kuma Iran a kan masu zabe a zaben majalisun dokokin kasar da ya gabata.
Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran ta bayyana cewa a jiya jumma'a ne babban komandan dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran ya bada labarin cewa an fara wannan atisayin wanda shi ne irinsa na farko a tsibirin Qishq.
Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya kai ziyarar aiki a yau a kasar Turkiya.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasimi ya bayyana cewa dangantakar tattalin arziki tsakanin kasar Iran da kuma Iraqi tana tafiya kamar yadda ya dace duk tare da matsin lamaba wanda gwamnatin Amurka takewa kasar Iraqi.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Dr. Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, babu wani batun wata sabuwar tattaunawa a halin yanzu tsakanin kasar Iran da kuma Amurka.
Tarayyar Turai ta bayyana cewa tana aiki dare da rana don ganin sabon tsarin musayar kudade da harkokin kasuwanci tsakanin ta da Iran ya fara aiki.