Kasancewar Amurka A Siriya, Tun Farko Kuskure Ne_Iran
(last modified Sat, 22 Dec 2018 16:19:05 GMT )
Dec 22, 2018 16:19 UTC
  • Kasancewar Amurka A Siriya, Tun Farko Kuskure Ne_Iran

Kwanaki kadan bayan da Shugaba Donald Trump na AMurka ya bayyana shirin janye sojojin kasarsa daga Siriya, Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta bayyana hakan da cewa, tun farko dama kasancewar sojojin na Amurka a Siriyar kuskure ne.

Da yake sanar da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, Bahram Qassemi, ya bayyana cewa kasancewar dakarun na Amurka a yankin kure ne dama tun farko, sannan ba kan gaskia ne ba, hasali ma haddasa fitina ne.

Mista Qassemi, ya kara da cewa sanya kasar AMurka a yankin musamman a Siriya, hadassa rikici da matsalar rashin tsaro. 

A ranar Laraba data gabata ne shugaba Trump na Amurka ya sanar da janye sojojin kasarsa kimanin 2,000 dake arewa maso gabashin Siriya wandanda ke dafawa mayakan kurdawa baya.

Kafofin yada labarai a Iran dai sun bayyana matakin na janye sojojin AMurka daga Siriya a matsayin babbar nasara ga Siriya, dama kawayenta Iran din da kuma Rasha dake goyan bayan gwamnatin Bashar Al-Assad.

Saidai wasu kasashen yamma ciki harda abokan kawancen da Amurkar ke jagoranta sun nuna damuwa akan wannan matakin na janyewa daga Siriyar wanda suka ce zai kara karawa Iran da Rasha dama gwamnatin Damascos karfi ne.