-
Ayatollah Khatami: 'Yan Siyasar Iran Abokan Juna Ne Bayan Zabe
May 26, 2017 13:38Limamin da ya jagoranci sallar jumma'a a nan Tehran Ayatollah Ahmad Khatami ya yi kira ga yan siyasa a kasar Iran, bayan zabe da kuma bayyana wadanda suka sami nasara, da su maida kasa da ke tsakaninsu kafin zabe ya zama abota da aiki tare.
-
Iran: Yerjejeniyar Makamai Ba Zasu Bawa Kasar Saudia Tsaron Da Take Bukata Ba
May 26, 2017 13:22ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zareef ya bayyana cewa yerjejeniyoyin sayan makamai wadanda kasar Saudia ta kulla da Amurka ba zasu samar mata da tsaro da zaman lafiya a kasar ba.
-
Iran: Za A Fara Neman Ganin Jaririn Wata Ramadan Da Yammacin Yau Juma'a
May 26, 2017 02:11Shugaban cibiyar neman jaririn watan a gundumar Yazd ya sanar da tura kungiyoyin kwararru hudu zuwa sassan daban-daban na gundumar domin ganin jaririn watan.
-
Iran Ta Sanar Da Sake Gina Wata Masana'antar Kera Makamai Masu Linzami Na Karkashin Kasa
May 25, 2017 13:40Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran sun sanar da cewar za su ci gaba da karfafa irin karfin da suke da shi na kariya musamman a fagen makamai masu linzami suna masu sanar da kera wata masana'anta ta uku ta karkashin kasa ta kera makamai masu linzami.
-
Iran Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Sayar Da Makamai Ga 'Masu Goyon Bayan Ta'addanci"
May 23, 2017 01:23Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kirayi Amurka da ta yi watsi da siyasarta ta neman hada fada, tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashe, sanya tsoron Iran cikin zukatan kasashe da kuma sayar da makamai masu hatsari da manyan masu goyon bayan ayyukan ta'addanci a duniya.
-
Zarif: Zai Fi Kyau Ga Trump Ya Kula Kada A Sake Kai Musu Hari Irin Na 9/11
May 21, 2017 12:49Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif, ya ja hankalin shugaban kasar Amurka Donald Trump da cewa, da zai fi a gare shi a ziyarar da yake yi a saudiyya ya tabbatar da cewa sun daddale da mahukuntan kasar, domin kada a sake kai ma Amurka wani hari makamancin 9/11.
-
Dan Kasar Iran Ya Zo Na Daya A Gasar Kur’ani Ta Duniya A Malaysia
May 21, 2017 12:48Makarancin kur'ani mai tsarki dan kasar Iran Hamed Alizadeh ya zo na daya a gasar karatun kur'ani mai tsarki ta duniya karo na 59 a kasar Malaysia .
-
Shugabanin Kasashen Duniya Na Ci Gaba Da Yiwa Shugaba Ruhani Murnar Samun Nasara A Zabe
May 21, 2017 03:04Shugaban Kasar Faransa Emmaniel Macron ya aike da sakon murna ga Shugaban kasar Iran Dr Hasan Ruhani dangane da nasarar da ya samu a zaben Shugabancin kasar
-
Vilayati:Halartar Mutane Shine Tushen Karfin Jumhoriyar Musulinci ta Iran
May 21, 2017 03:03Shugaban Cibiyar Binciken dubaru na Majalisar fayyace maslahar tsarin musulinci na Iran ya ce daga cikin mahiman abubwan da suka sanya kasar Iran ta tsaya da kafafunta shine kasancewar Mutane a fage mababbanta kama daga fagen kare kasa a kallafaffen yaki, aiyukan gina kasa da kuma siyasa
-
Shuwagabannin Kasashen Rasha Da Siria Sun Taya Shugaban Ruhani Murnan Sake Zabensa
May 20, 2017 12:37Shuwagabannin kasashen Rasha da Syria sun aike da sakon taya murna ga shugaban kasar Iran Dr Hassan Roohani kan sake zabensa a karo na biyu wanda mutanen kasar Iran suka yi a zaben jiya jumma'a.