-
Ruhani:Kasar Iran Tana Bukatar Hulda Mai Mutunci Da Sauran Kasashen Duniya
May 20, 2017 12:17Shugaban kasar Iran Dr Hassan Roohani ya bayyana cewa mutanen kasar Iran sun nunawa duniya cewa sun zabi tafarkin zaman lafiya da kuma mutunci, nesa da tashe tashen hankula a huldansu da sauran kasashen duniya.
-
Jagoran Juyin Juya Hali Ya Yaba Da Fitowar Mutanen Iran A Zaben Jiya Jumma'a
May 20, 2017 11:30Jagoran juyin juya halin musulunci Aya. Sayyeed Aliyul -Khaminae ya yabawa mutanen kasar Iran kan yadda suka fito konsu da korkotansu don halartar zaben shugaban kasa da sauran zabubbuka na kasar a jiya jumma'a.
-
Dr Hasan Ruhani Ya Sake Lashe Zaben Shugabancin Kasar Iran
May 20, 2017 07:20Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Iran ta sanar da Dr Hasan Ruhani a matsayin dan takarar shugabancin kasar da ya lashe zaben shugaban kasar da mafi rinjayen kuri'u.
-
Yadda Iraniyawa Suka Nuna Da'a Da Kishin Kasa A Yayin Zabe
May 20, 2017 00:47A yayin da al'ummar Iran ke dakon sakamakon zaben da aka kada kuri'arsa a jiya Juma'a, wani batu da ya dau hankalin duniya shi ne yadda Iraniyawan suka nuna da'a da kishin kasa a zaben.
-
Sakamakon Farko Na Zaben Shugaban Kasar Iran: Shugaba Hassan ya sami kuri'u miliyan 22,796,468
May 20, 2017 00:33Hukumar Zaben, da ta sanar da sakamakon ta ce; ya zuwa yanzu Shugaba Hassan Rauhani yana kan gaba da kuri'a Miliyan 14.
-
Rahotanni: An Sami Gagarumar Fitowar Al'ummar Iran A Yayin Zaben Shugaban Kasa Na Yau
May 19, 2017 13:24Rahotanni daga suke fitowa daga bangarori daban-daban na kasar Iran musamman a manyan biranen kasar na nuni da cewa miliyoyin al'ummar kasar sun fito don kada kuri'arsu a zaben shugaban kasar da na 'yan majalisun kananan hukumomi da ake gudanarwa a yau din nan Juma'a lamarin da ya sanya aka kara sa'oi kan lokacin da ya kamata a rufe rumfunan zaben.
-
Ayat. Kermani: Wajibi Ne Shugaban Da Aka Zaba Ya Kusa Da Talakawa Da Girmama Koyarwar Juyi
May 19, 2017 13:24Wanda ya jagoranci sallar juma'ar birnin Tehran Ayatullah Mohammad Ali Movahedi Kermani ya bayyana cewar wajibi ne shugaban da za a zaba a matsayin sabon shugaban kasar Iran ya zama mai kula da talakawa da kuma kiyaye koyarwar juyin juya halin Musulunci, yana mai jinjinawa al'ummar Iran saboda irin gagarumar fitowar da suka yi.
-
Iran Tana Sanya Ido Kan Duk Wani Kai Komon Makiyanta
May 19, 2017 07:32Minista mai kula da harkar tattara bayanan sirri a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Jami'an tsaron kasar Iran a shirye suke su maida da martani kan duk wani makircin da makiya zasu nemi aiwatarwa kan kasarsu.
-
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Kada Kuri'arsa
May 19, 2017 01:19Da kimanin karfe 8:00 agogon kasar Iran ne jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya kada kuri'arsa a zaben shugaban kasa da kuma na kananan hukumomi da ake gudanarwa yau a kasar.
-
An Fara Gudanar da Zabukan Shugaban Kasa Da Kananan Hukumomi A Iran
May 19, 2017 01:12An fara gudanar da zabukan shugaban kasa da majalisun kanan hukumomi na Iran, inda miliyoyin jama'a ke ci gaba da shiga cikin layuka a runfunan zabe suna kada kuri'unsu.