An Fara Gudanar da Zabukan Shugaban Kasa Da Kananan Hukumomi A Iran
(last modified Fri, 19 May 2017 05:42:12 GMT )
May 19, 2017 05:42 UTC
  • An Fara Gudanar da Zabukan Shugaban Kasa Da Kananan Hukumomi A Iran

An fara gudanar da zabukan shugaban kasa da majalisun kanan hukumomi na Iran, inda miliyoyin jama'a ke ci gaba da shiga cikin layuka a runfunan zabe suna kada kuri'unsu.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Iran Abdul-ridha Rahmani Fadhli ya bayyana cewa, an fara bude runfunan zaben karfe 8:00 daiai kamar yadda aka tsara, inda tun kafin lokacin jama'a sun fara isa wuraren.

Wannan dai shi ne akro na 12 da ake gudanar da zaben shugaban kasa a Iran tun bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar a shekara ta 1979.

Kimanin mutane miliyan 56 da dubu 410 ne suka cancanci kada kuri'a a kasar ta Iran, baya cikin Iran, ana gudanar da wannan zabe a kasashe 102, inda a can ma Iraniyawa suke kada kuri'unsu.