Iran Tana Sanya Ido Kan Duk Wani Kai Komon Makiyanta
Minista mai kula da harkar tattara bayanan sirri a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Jami'an tsaron kasar Iran a shirye suke su maida da martani kan duk wani makircin da makiya zasu nemi aiwatarwa kan kasarsu.
A ganawarsa da manema labarai kafin kada kuri'arsa a zabukan da ake gudanarwa a duk fadin kasar Iran a yau Juma'a: Minista mai kula da harkar tattara bayanan sirri a Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sayyid Mahmud Alawi ya bayyana cewa: Jami'an tsaron Iran suna fadake tare da sanya ido kan duk wani motsin makiya lamarin da zai basu damar tabbatar da tsaro da zaman lafiya a duk ranakun gudanar da zabuka a cikin kasar Iran.
A yau ne Juma'a ne ake gudanar da zabukan shugaban kasa da na kananan hukumomi a duk fadin kasar Iran, kuma miliyoyin mutane suna ci gaba da dafifin zuwa rumfunar zabe domin kada kuri'unsu da nufin zabarwa kansu shugabanni na gari.