Dan Adawa Felix Tshisekedi, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa A DR Congo
Dan takaran adawa a jamhuriya Demokuradiyyar Congo, Félix Tshisekedi, ya kafa tarihi, inda ya lashe zaben shugaban kasar tun a zagayen farko.
A sakamakon wucin gadi data fitar a cikin daren jiya, hukumar zaben kasar ta CENI, ta ayyana Félix Tshisekedi, a matsayin wanda ya lashe zaben da kashi 38,57% na yawan kuri'un da aka kada.
Mista Tsisekedi, ya lashe zaben shugaban kasar na ranar 30 ga watan Disamba da ya shude, gaban manyan 'yan takaran da suka hada da Martin Fayulu, shi ma na adawa da kuma Emmanuel Ramazani Shadary, dan takaran jam'iyyar FCC, mai mulki, kamar yadda shugaban hukumar zaben kasar Corneille Nangaa ya sanar.
'Yan takara 21 ne suka fafata a zaben, wanda ya samu fitowar jama'a da 47,46%.
Kotun tsarin mulkin kasar ce take da alhakin bayyana sakamakon dindindin na zaben shugaban kasa.
A cikin tsarin kudin zabe na kasar, kafin a dage sanar da sakamakon wucin gadi da kwanaki hudu, an tsara rantsar da shugaban kasa a ranar 18 ga watan Janairu.
Félix Tshisekedi, dan shekaru 55, na da 'ya 'ya biyar, kuma ya yi suna ne kasancewarsa da ga jagoran 'yan adawa na kasar mai rasuwa Etienne Tshisekedi.
A watan Maris na 2017, bayan rasuwar mahaifinsa aka nada shi a matsayin shugaban jam'iyyar UDPS, kafin daga bisani a tsaida shi a matsayin dan takaran shugaban kasa na Jam'iyyar.
Kusan dai wannan shi ne karo na farko a tarihin wannan kasa ta DR Congo da wani shugaba zai mika mulki a cikin ruwan sanyi, tun bayan data samu 'yanci kai a cikin shekara 1960.