Dr Hasan Ruhani Ya Sake Lashe Zaben Shugabancin Kasar Iran
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Iran ta sanar da Dr Hasan Ruhani a matsayin dan takarar shugabancin kasar da ya lashe zaben shugaban kasar da mafi rinjayen kuri'u.
A taron manema labarai da ya gudanar dazu-dazun nan a yau Asabar: Ministan harkokin cikin gidan kasar Iran Abdolreza Rahmanifazli ya sanar da cewa: A zaben shugabancin kasar Iran da ya gudanar a jiya Juma'a, an samu yawan kuri'u 41,220,131, inda Dr Hasan Ruhani ya samu kuri'u da yawansu suka kai 23,549,616, lamarin da ya ba shi nasarar sake lashe kujerar shugabancin kasar ta Iran.
Rahmanifazli ya kara da cewa: Sayyid Ibrahim Ra'isi Sadat da ya zo a matsayin biyu, ya samu yawan kuri'u 15,786,449, yayin da Mustapha Agha Mir Salim ya samu kuri'u 478,215 a matsayin na uku, sannan Mustapha Hashimi Tabah ya samu kuri'u 215,450 a matsayi na hudu, kuma na karshe a tsakanin 'yan takarar shugabancin kasar ta Iran.