Shuwagabannin Kasashen Rasha Da Siria Sun Taya Shugaban Ruhani Murnan Sake Zabensa
https://parstoday.ir/ha/news/iran-i20552-shuwagabannin_kasashen_rasha_da_siria_sun_taya_shugaban_ruhani_murnan_sake_zabensa
Shuwagabannin kasashen Rasha da Syria sun aike da sakon taya murna ga shugaban kasar Iran Dr Hassan Roohani kan sake zabensa a karo na biyu wanda mutanen kasar Iran suka yi a zaben jiya jumma'a.
(last modified 2019-03-07T02:07:59+00:00 )
May 20, 2017 12:37 UTC
  • Shuwagabannin Kasashen Rasha Da Siria Sun Taya Shugaban Ruhani Murnan Sake Zabensa

Shuwagabannin kasashen Rasha da Syria sun aike da sakon taya murna ga shugaban kasar Iran Dr Hassan Roohani kan sake zabensa a karo na biyu wanda mutanen kasar Iran suka yi a zaben jiya jumma'a.

Tashar lelevision ta Presstv a nan tehran ta nakalto Fadar Crimline tana fadar haka a wani sakon Telegaram wanda shugaba Putin ya aikewa Ruhana bayan an bayyana sakamakon zaben shugaban kasar na jiya.

Putin ya kara da cewa mutanen iran sun nuna a wannan zaben kan cewa sun amince da ayyukan ci gaba da kuma tabbatar da zaman lafiya wanda Iran da kawayenta suke aiwatarwa a yankin.

Shugaba ya kammala da cewa yana fatan dukkam yerjeniyoyin da kasar Rasha ta cimma da Iran a zagaye na farko na shugabancin Roohani za'a aikwatar da su a zagaye na biyu n ashugabancin kasar.

A wani bangaren kuma shugaban kasar Syria Bashar Al-asad ya aike da sakon  tara murna ga shugaba Roohani bayan an bayyana sakamankon zaben shugaban kasa a safiyar yau Asabar.

Shugaban ya kara da cewa mutanen kasar Iran a zaben na jiya jumma'a sun sake bawa shugaba Ruhani damar ci gaba da ayyukan tabbatar da zaman lafiya a yankin da ma duniya gaba daya.