Vilayati:Halartar Mutane Shine Tushen Karfin Jumhoriyar Musulinci ta Iran
Shugaban Cibiyar Binciken dubaru na Majalisar fayyace maslahar tsarin musulinci na Iran ya ce daga cikin mahiman abubwan da suka sanya kasar Iran ta tsaya da kafafunta shine kasancewar Mutane a fage mababbanta kama daga fagen kare kasa a kallafaffen yaki, aiyukan gina kasa da kuma siyasa
A yayin da yake hira da tashar Telbijin din kasar a daren jiya Assabar, Ali Akbar Vilayati Shugaban Cibiyar Binciken dubaru na Majalisar fayyace maslahar tsarin musulinci na Iran ya ce halartar Mutane sama da kashi 70% daga cikin mutanan da suka caccanci kada kuri'a a cikin kasar da kuma yadda Iraniyawa dake zauna a kasashe wajen suka gudanar da zabe a sama da kasashe 100, shi ke nuna yadda kasar ta Iran ta ci gaba da tsakanin kasashen Duniya da yankin.
Har ila yau Ali Akbar Vilayati ya kara da cewa fagen siyasa da kuma yadda Al'ummar kasar ta karbi wannan zabe shi ke nuna hadin kan da Al'ummar kasar ke da shi tare kuma da kare juyin juya halin musulincin kasar bayan kusan shekaru 40 da aukuwarsa
Shugaban Cibiyar Binciken dubaru na Majalisar fayyace maslahar tsarin musulinci na Iran ya kara da cewa Hadin kai da Al'ummar kasar ke shi, shi ke karya lagon makiyan kasar, kuma yadda Al'ummar kasar suka fito kwansu da kwalkwatarsu wajen ka'ada kuri'a ya kara fisata makiya sannan kuma shi ke nuna cewa 'yan ta'addar da suka shigo yankin da kuma sharrin Sahayoniya bisa goyon bayan Amurka da wadanda suka karkata zuwa gare su a yankin za su kwashi kashin su a hannu a duk lokacin da suka kuskure wajen kawo wa kasar hari.