Pars Today
Rahotanni daga Iraki na cewa jami'an 'yan sanda hudu ne suka rasa rayukansu a wasu jerin hare haren bam a arewacin Bagadaza.
Shugaban kungiyar hizbullah ta kasar Labnon ya ce haramtacciyar kasar Isra'ila ta sha kashi a kasar Siriya
A jiya Juma'a ne sojojin na Sahayoniya su ka kai samame a yankin kogin Jordan inda us ka yi awon gaba da Palasdianwa 4
Majiyar hukumar leken asiri na sojan kasar ta Iraki ce ta sanar da gano ramin a garin Fallujah da ke gundumar Anbar
Kungiyar injiniyoyi na kasar Sudan sun bayyana adawarsu da gwamnatin shugaba Umar hassan Albshir a yau Alhamis.
Jakadan kasar Amurka na musamman a kasar Afganistan sannan mai wakiltan kasar a tattaunawar da ke gudana a halin yanzu a birnin Doha na kasar Qatar tare da kungiyar Taliban ya ce tattaunawarsu ta shiga kwana na hudu a yau Alhamis.
Sojojin Kasar Yemen ne su ka sanar da kashe 'yan koren Saudiyya 30 a wani hari da su ka kai musu a gundumar Jizan da ke kan iyaka
Majalisar wakilai a kasar Amurka ta amince da wani kuduri wanda zai sa gwamnatin shugaban Trump ta kara kakabawa gwamnatin kasar Siriya takunkuman tattalin arziki.
Ministan tsaron kasar Burtaniya ya bada sanarwan cewa gwamnatinsa zata janye rabin jiragen yakin kasar wadanda suka aikin abinda ya kira zaman lafiya a kasar Siriya zuwa gida.
Sojojinn kasar Lebanon sun bada sanarwan kama mutumin da ake tuhuma da kokarin kashe wani babban jami'an kungiyar gwagwarmaya ta Palasdinawa HAMAS a kasar Lebanon