Yemen: "Yan Koren Saudiyya 30 Sun Halaka
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i34929-yemen_yan_koren_saudiyya_30_sun_halaka
Sojojin Kasar Yemen ne su ka sanar da kashe 'yan koren Saudiyya 30 a wani hari da su ka kai musu a gundumar Jizan da ke kan iyaka
(last modified 2019-01-24T09:03:44+00:00 )
Jan 24, 2019 09:03 UTC
  • Yemen:

Sojojin Kasar Yemen ne su ka sanar da kashe 'yan koren Saudiyya 30 a wani hari da su ka kai musu a gundumar Jizan da ke kan iyaka

Sojoji da kuma dakarun sa kai na kasar ta Yemen sun kuma kwace iko da wasu sansanoni na sojojin Saudiyya da ke "Jabalun-Nar' a cikin gudunmar ta Jizan, tare kuma da daukar ganiyar makamai da kayan yaki da suek ciki

Tare da cewa kasar Yemen tana a karkashin killacewar kawancen yaki da Saudiyya take jagoranta, ta sama da kasa da ruwa, amma duk da haka, sojoji da dakarun sa kai na kasar suna kara karfi

Saudiyya ta shelanta yaki ne akan kasar Yemen tun a cikin watan Maris na 2015, tare da killace kasar ta sama da ruwa da kasa.

Fiye da mutane 14,000 ne aka tabbatar da sun mutu a tsawon shekaru 4 na yakin kasar Yemen, yayin da wasu dubun dubata su ka jikkata.