Injiniyoyi A Kasar Sudan Sun Bayyana Adawarsu Da Gwamnatin Shugaba Albashir
Kungiyar injiniyoyi na kasar Sudan sun bayyana adawarsu da gwamnatin shugaba Umar hassan Albshir a yau Alhamis.
Tashar talabijin ta Aljazeera na kasar Qatar ta nakalti injiniyoyin suna taro a gaban ofishin kungiyar dake birnin Khartum babban birnin kasar a yau Alhamis, inda suke rike da kellaye dauke da rubutu na bukatar shugaba Albashir ya yi murabus.
Majiyar jami'an tsaro da kasar ta Sudan ta bayyana cewa jami'an tsaro sun yi amfani da karfi don tarwatsa masu injiniyoyin. Sun yi amfani da kulake masu wutan lantarki da kuma hayaki mai sa hawaye don tarwatsa su. Banda haka sun kama wasu injinoyoyin .
Tun ranar 19 ga watan Jenerun da muke ciki ne mutanen kasar Sudan suka fara zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da tsadar kayakin bukatun yau da kullum a kasar ta Sudan.
Amma daga baya zanga-zangar ta rikide ta zama na neman murabus na shugaban kasar ta Sudan Umar Hassan Albahir wanda ya share fiye da shekaru 20 yana mulkin kasar.