-
Martanin Hukumar kare Hakin Bil-Adama A Kan Kame Dan Takarar Shugaban Kasa A Masar
Jan 25, 2018 02:52A yayin da Gwamnatin kasar Masar ta kame Sami Hafez Anan dan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, hukumar kare hakin bil-adama ta MDD ta kirayi mahukuntan kasar ta Masar da suka guji yin katsa-landan a al'amuran zabe.
-
Italiya Ta Yi Kira Da A Taimaka Wa Kasashen Afirka Su Magance Matsalar 'Yan Ci-Rani.
Jan 24, 2018 15:38Pira ministan kasar Italiya Paolo Gentiloni ne ya yi kiran kasashe duniya da su taimaka domin bunkasa tattalin arzikin nahiyar Afirka da hakan zai magance matsalar 'yan ci-rani.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Gudanar Da Kwaskwarima A Fagen Ayyukan Dakarunta
Jan 23, 2018 15:34Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bai wa dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na Majalisar damar amfani da makamai wajen kare kansu.
-
Siriya : Faransa Ta Sanya Takunkumi Kan Wasu Kamfanoni Da Jami'ai 25
Jan 23, 2018 07:47Kasar Faransa ta sanar da kakaba takunkumi kan wasu Cibiyoyi da jami'ai su 25 kan zargin taimakawa shirin Siriya na sarafawa da kuma kera makamai masu guba.
-
Venezuela Ta Yi Allawadai Da Takunkumin EU
Jan 23, 2018 07:47Kasar Venezuela ta fitar da sanarwar yin allawadai da sabon takunkumin da kungiyar tarayya turai ta kakaba mata.
-
Iran Ta Mayar Da Martani Ga Kalaman Ministan Harkokin Wajen Faransa
Jan 23, 2018 01:44Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewar ba za ta yi wata tattaunawa don cimma yarjejeniyar kan shirinta na makamai masu linzami da kasashen Turai ba tana mai cewa shirinta na kare kai lamari ne da ya shafi cikin gidanta da ba za ta taba bari wani ya tsoma mata baki cikinsa ba.
-
Sabuwar Siyasar Tsaron Kasar Amurka Da Zargi Maras Tushe Kan Kasar Iran
Jan 22, 2018 23:19A ranar Juma'ar da ta gabata ce sakataren tsaron kasar Amurka Jim Mattis ya gabatar da abin da suke kira "Dabarun Tsaron Kasar Amurka Na Shekara ta 2018", inda ya bayyana kasashen Rasha Da China a matsayin babbar barazana ga Amurka da kawayenta a fage na kasa da kasa, sannan a yankin Gabas ta tsakiya da Asiya kuma ya bayyana Iran da Koriya ta Arewa a matsayin manyan kalubalen da Amurkan take fuskanta a yankin.
-
Faransa Ta Bukaci Taron Gaggawa Na Kwamitin Tsaron MDD Game Da Siriya
Jan 21, 2018 15:32Bayan shigar kasar Turkiya a yankin Ifrin na arewacin kasar Siriya, kasar Faransa ta bukaci taron gaggauwa na kwamitin tsaron MDD
-
MDD Ta Bukaci Taimakon Dala Biliyan Uku Domin Taimakawa Al'ummar Kasar Yemen
Jan 21, 2018 15:31Majalisar dinkin duniya ta bukaci taimakon dala bilyan uku domin taimakawa al'ummar kasar Yemen dake cikin mawuyacin hali sakamakon hare-haren wuce gona da iri na masarautar saudiya.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bayyana Damuwarta Kan Rikicin Yankin Afrin Na Kasar Siriya
Jan 21, 2018 03:40Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwarta kan rikicin da ya kunno kai tsakanin sojojin Turkiyya da mayakan kurdawan kasar Siriya a yankin Afrin da ke arewacin kasar ta Siriya.