Venezuela Ta Yi Allawadai Da Takunkumin EU
Jan 23, 2018 11:17 UTC
Kasar Venezuela ta fitar da sanarwar yin allawadai da sabon takunkumin da kungiyar tarayya turai ta kakaba mata.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta danganta takunkumin da shishigi cikin al'amuran cikin gidan kasar, wanda hakan ya sabawa yarjejeniyar MDD.
Mahukuntan Caracas sun ce wannan matakin na EU da akwai hannun gwamnatin Amurka a ciki.
Mataimakin shugaban kasar Venezuela dai ya bukaci gwamatin kasar da ta dau mataki makamancin wannan kan gwamnatocin kasashen Turan.
Sabon takunkumin da kungiyar ta EU ta dauka kan kasar ta Venezuwala ya shafi wasu mayan jami'an gwamnatin kasar ciki har da mataimakin shugaba Nicolas Maduro.
Tags