Iran Ta Mayar Da Martani Ga Kalaman Ministan Harkokin Wajen Faransa
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewar ba za ta yi wata tattaunawa don cimma yarjejeniyar kan shirinta na makamai masu linzami da kasashen Turai ba tana mai cewa shirinta na kare kai lamari ne da ya shafi cikin gidanta da ba za ta taba bari wani ya tsoma mata baki cikinsa ba.
Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen Iran din ne, Bahram Qassemi, ya bayyana hakan a yayin da yake mayar da martani ga kalaman ministan harkokin wajen kasar Faransa, Jean-Yves Le Drian, kan shirin makamai masu linzami da kuma siyasar Iran kan kasashen yankin Gabas ta tsakiya inda ya ce matsayar Iran kan makamanta masu linzami da kuma siyasarta kan kasashen yankin wata matsaya ce da take a fili.
Yayin da yake magana dangane da ziyarar da ake sa ran ministan harkokin wajen Faransan zai kawo nan Iran, kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya ce har ya zuwa yanzu ba a ma tsayar da abubuwan da za a tattauna yayin ziyarar ministan harkokin wajen Faransan, yana mai sake jaddada cewa akwai bambanci tsakanin tattaunawa da kuma musayen ra'ayi.
A jiya Litinin ne dai ministan harkokin wajen Faransan, Jean-Yves Le Drian, a wata ganawa da yayi da manema labarai a birninBrussels na kasar Belgium ya zargi Iran da rashin mutumta kudurin kwamitin tsaro kan shirinta na makamai masu linzami masu cin dogon zango da kuma abin da ya kira katsalandan da Iran ta ke yi a kasashen yankin Gabas ta tsakiya wanda ya ce za su ci gaba da matsin lamba wa Iran kan wadannan batutuwa.