Pars Today
Shugaba Vladimir Putin, na Rasha, ya sanar a yau Asabar da janye kasarsa daga yarjejeniyar takaita kera makamman nukiliya ta INF dake tsakanin Rashar da Amurka.
Majiyar shari'a a kasar Rasha ta bada sanarwan cewa an yanke hukunci na zaman kaso mai tsawo ga wasu yayan kungiyan yan ta'adda ta Daesh su biyar.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a daren jiya juma'a, ma'aikatar harakokin wajen Rasha ta ce kasar Amurka na amfani da 'yan ta'adda domin cimma manufofinta a kasar Siriya.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya sanar a daren jiya juma'a cewa kasashe 28 na kungiyar tarayyar Turai sun yanke shawarar ko wata kasa daga cikin manbobinta ta bayyana goyon bayanta ga Juan Guaido shugaban 'yan adawar kasar Venezula a matsayin shugaban kasa ficin gadi.
Jami'an Siyasa na tarayyar Turai sun yi maraba da kafa gwamnati a kasar Lebanon.
Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bada sanarwan ficewar kasar Amurka daga yerjejeniyar hana kirar makamai masu linzamin masu kaiwa matsakaicin zanga tsakaninta na Rasha.
Kungiyar tarayya ta kafa wani sabon shiri na cinikaya da Iran, wanda zai kaucewa takunkuman da Amurka ta kakaba wa Iran din bayan data fice daga yarjejeniyar nukiliya.
Dubban mutanen kasar Venezuela ne suka fito kan tituna a birane da dama na kasar Inda suke nuna goyon bayansu ga shugaban Nicola Madorus a yau Alhamis.
Shugabannin Kungiyar Tarayyar Turai EU, sun jaddada cewa ba za su sake ganawa da Birtaniya, kan bukatar yi wa yarjejeniyar Brexit kwaskwarima ba.
Asusun kananen yara na MDD Unicef ya ce yakin dake wakana a kasar yemen ya yi sanadiyar mutuwa da jikkatar kananan yara dubu 6 da 700