Pars Today
Wani sakamakon sauraron ra'ayin jama'a ya nuna yadda mafi rinjayen mutanen kasar Venezuela suke adawa da katsalandan da Amurka take yi a harkokin cikin kasarsu
Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro, ya bayyana cewa a shirye yake ya tattauna da 'yan adawa, domin tattauna makomar kasar.
Jami'an tsaron gabar ruwa a Djibouti, sun ce bakin haure 28 ne suka rasa rayukansu bayan kifewar wasu kwale kwale biyu a teku kusa da Djibouti.
Babban mai shigar da kara na gwamnatin Venezuela, ya bukaci kotun kolin kasar data haramta wa jagoran 'yan adawa na kasar Juan Guaido fita kasar da kuma toshe asusunsa na banki.
Kasashen China da Rasha sunyi allawadai da sabbin takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasar Venezuela.
Wata cibiyan bincike a kasar Burtaniya ta bada sanarwan cewa gwamnatin kasar ta yi Asarar fam billiyon 17 tun lokacinda ta fara kokarin ficewa daga tarayyar Turai a shekara ta 2016.
A Philippines, mutum 18 ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan wasu jerin hare hare da aka kai kan wata coci dake yankin Jolo.
Kasar Venezuella ta yi watsi da wa'addin da wasu kasashen turai suka bata na ta kira zabe cikin kwanaki takwas ko kuma su amince da jagoran 'yan adawa na kasar a matsyin shugaban riko na kasar.
Yayin da 'Yan adawa da dokar haraji ke gudanar da zanga-zanga a ranar assabar ta 11, 'yan sanda sun yi amfanin da karfi wajen tarwatsa zanga-zangar a kasar Faransa.
Babban bankin kasar Birtaniya ya rike kudin Gwamnatin Venezuela bisa wasicin kasar Amurka