Philippines : Mutum 18 Sun Mutu A Wani Hari Kan Coci
A Philippines, mutum 18 ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan wasu jerin hare hare da aka kai kan wata coci dake yankin Jolo.
Bam din na farko, ya tashi ne a cikin cocin a daidai lokacin da ake gudanar da ibadar ranar Lahadi, a yayin da bam din na biyu ya fashe, wajen cocin, a daidai lokacin sojoji ke isowa wajen.
Daga cikin wadanda jerin hare haren ya rusa dasu akwai sojoji biyar, da kuma fararen hula 12, da kuma raunata wasu 83.
Saidai shugaban 'yan sanda yankin ya ce mutum 20 suka mutu a jerin hare haren, sannan kuma wasu 81 suka raunana.
Tuni dai gwamnatin kasar ta bakin kakakin shugaban kasar, ta yi allawai da harin tana mai danganta shi dana ta'addanci, a yayin da kuma mahukunatan kasar ke dora alhakin harin kan gungun islama na Abu Sayyaf a kasar.