Bakin Haure 28 Sun Mutu A Kifewar Kwale-kwale A Djibouti
https://parstoday.ir/ha/news/world-i35008-bakin_haure_28_sun_mutu_a_kifewar_kwale_kwale_a_djibouti
Jami'an tsaron gabar ruwa a Djibouti, sun ce bakin haure 28 ne suka rasa rayukansu bayan kifewar wasu kwale kwale biyu a teku kusa da Djibouti.
(last modified 2019-01-30T10:10:00+00:00 )
Jan 30, 2019 10:10 UTC
  • Bakin Haure 28 Sun Mutu A Kifewar Kwale-kwale A Djibouti

Jami'an tsaron gabar ruwa a Djibouti, sun ce bakin haure 28 ne suka rasa rayukansu bayan kifewar wasu kwale kwale biyu a teku kusa da Djibouti.

Ko baya ga hakan rahotanni sun nuna cewa akwai wasu gomman mutane da ake ci gaba da nema bayan kifewar kwale kwalen.

Tunda farko dai shugaban hukumar kula da bakin haure ta MDD, OIM a kasar ta Djibouti, ya ce an tsamo gawarwakin mutum biyar, sai kuma da safiyar yau Laraba inda aka gano tsamo wasu gawarwaki 23.

Nutsewar kwale kwalen ta auku ne a ranar Talata, mintuna talatin bayan da kwale kwalen shake da bakin haure ya bar gabar zuwan Djibouti, inda ya doshi kasar Yemen.