Birtaniya Ta Rike Dala Billiyon 1.2 na Kasar Venezuela
Babban bankin kasar Birtaniya ya rike kudin Gwamnatin Venezuela bisa wasicin kasar Amurka
Kafar watsa labaran Amurka Bloomberg a jiya Assabar ta habarta cewa babban bankin kasar Birtaniya ya yi watsi da bukatar shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro na mayarwa kasar sa da kudin da ta ajiye a bankin da ya kai dala billiyon 1.2 da kuma yawan zinarin dake jibke a Bankin.
Rahoton ya ce ganawar da jami'an kasar Amurka suka yi da suka hada da Mike Pompeo saktaren harakokin wajen Amurka da John R. Bolton mai bawa shugaban Amurka shawara kan harakokin tsaro da takwarorinsu na kasar Birtaniya shi ne dalilin da ya sanya Bankin ta ki amincewa da bukatar gwamnatin ta Venezuela.
Har ila yau rahoton ya ce gwamnatin Amurka na kokarin meka wadannan kudade ga shugaban 'yan adawan na Venezula da suka kira a matsayin shugaban kasar.
A halin da ake ciki, gwamnatin kasar Venezuela nada ajiya kudi da suka kai billiyon takwas a kasashen waje, daga ciki akwai biliyon 1.2 a kasar Birtaniya.
ko baya ga kasar Birtaniya, kasar Turkiya nada cikin kasashen da Venezuela ke ajiye kudaden a can, kuma a halin da ake ciki yanzu, kasar Amurka na yin barazana da matsin lamba ga mahukuntan na birnin Ankara ta yadda kadda su mika ajiyar kasar Venezuela ga shugaba Madoro.