Venezuela : Maduro Na Ci Gaba Da Samun Goyan Baya
Dubban mutanen kasar Venezuela ne suka fito kan tituna a birane da dama na kasar Inda suke nuna goyon bayansu ga shugaban Nicola Madorus a yau Alhamis.
Majiyar MJMI ta bayyana cewa dubban mutane ne suka fito a babbam birnin kasar da kuma wasu birani wadanda suka hada da Falcón suna nuna goyon bayansu ga shugaban kasar sannan suna allawadai da juyin mulki a kasar.
A wani labarin kuma jamalisar tarayyar turai ta amince da Juan Guaido wanda ya nada kansa shugaban yan adawar kasat ta Venezuela a matsayin halattacen shugaban kasar, sannan duk wata hulda da kasar sai ta hannunsa zasu yi.
Har'ila yau wasu labarai sun abayyana cewa shugaban kasar Amurka Donal Trump ya tattauna ta wayar tarko da shugaban yan adawan Juan Guaido inda ya tabbatar masa da goyon bayansa.
Sai kuma a shafinsa na Tweeter shugaban Amurka ya yi kira ga mutanen kasar Venezuela su yi borewa gwamnatin shuga Nicola Madorus.