Rasha Ta Yi Wastsi Da Yarjejeniyar Makamai Ta INF
(last modified Sat, 02 Feb 2019 14:25:08 GMT )
Feb 02, 2019 14:25 UTC
  • Rasha Ta Yi Wastsi Da Yarjejeniyar Makamai Ta INF

Shugaba Vladimir Putin, na Rasha, ya sanar a yau Asabar da janye kasarsa daga yarjejeniyar takaita kera makamman nukiliya ta INF dake tsakanin Rashar da Amurka.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Amurka ta sanar da janye jiki daga yarjejeniyar dake tsakanin kasashen biyu tun shekara 1987.

Da yake sanar da hakan a yayin wata ganawa da ministocin tsaro dana harkokin wajen kasarsa, shugaba Putin ya ce '' Amurka ta sanar da cewa ta janye daga yarjejeniyar, to mu ma munbi sahunta wajen ficewa daga yarjejeniyar.

Kasar Rasha ta ce ba zata kara hawa teburin tattaunawa ba kan yarjejeniyar makamai da Amurka ba, har sai Amurkar ta nuna da gaske take kan duk wata tattaunawa kan batun.

Yau Asabar ne matakin na Amurka ya fara aiki, inda za ta soma aiwatar da shirin janyewa daga yarjejeniyar baki daya, wanda za ta kammala cika sharuddan fita cikin wa’adin watanni 6.

Kasashen Amurka da Rashar dai na zargin junansu da keta yarjejeniyar. 

A shekarar 1987 shugaban Amurka Ronald Regan da takwaransa na tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev suka rattaba hannu kan yarjejeniyar wadda ta kunshi haramta kera makamai masu linzami, wadanda ke cin dogo da matsaikacin zango, cikin gudun tsiya idan an harba su.