-
Shugaban Gwamnatin Catalonia: Mun Sami Hakkin Zama Masu 'Yanci
Oct 02, 2017 03:42Carles Puigdemont wanda shi ne shugaban yankin na Catalonia ya fadi haka ne bayan sanar da sakamakon kuri'ar raba gardama a jiya lahadi.
-
Peter Ford: Kasashen Larabawa Da Na Yammacin Turai Ne Suka Karfafa Ta'addanci A Siriya
Oct 01, 2017 03:01Tsohon jakadar kasar Birtaniya a Siriya ya ce: Bakar siyasar wasu kasashen yammacin Turai da na kasashen Larabawan yankin tekun Pasha ita ce ta karfafa ayyukan ta'addancin kungiyar Da'ish a kasar Siriya.
-
'Yan Shi'a Na Gudanar Da Juyayin Ranar Tasu'a A Kasashe Daban-Daban Na Duniya
Sep 30, 2017 07:47Musulmi 'yan Shi'a a duk fadin duniya sun fara gudanar da ranar Tasu'a don tunawa da rana ta tara na watan Muharram rana guda kafin faruwar Waki'ar Karbala inda Imam Husain (a.s) da iyalai da sahabbansa suka yi shahada a Karbala.
-
MDD Za Ta Binciki Zargin Aikata Laifukan Yaki A Yemen
Sep 30, 2017 02:08Bayan shafe doguwar tattaunawa mai wuya, kwamitin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya, ya amunce da kudirin aikewa da wata tawagar kwararu na kasa da kasa don yin bincike kan zargin aikata laifukan yaki a kasar Yemen.
-
Rasha : Putin Na Ziyara A Turkiyya
Sep 28, 2017 12:59Shugaba Vladimir Putin na Rasha, zai gana da takwaransa na Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan a birnin Ankara, a yayin wata 'yar gajeriyar ziyara da ya ke a birnin Ankara.
-
MDD : Adadin 'Yan Rohingya A Bangaladash Ya Kai Rabin Milyan
Sep 28, 2017 11:02Majalisar Dinikin Duniya ta fitar da wani rahoto dake cewa, adadin 'yan gudun hijira Rohingya dake gujewa kisan kiyashin da ake musu a kasar Myammar ya haura rabin Miliyan.
-
Myanmar: Masu Binicke Na Majalisar Dinkin Duniya Za Su Shiga Yankin Musulumi
Sep 28, 2017 03:22Masu binciken sun sanar da cewa mai yiyuwa ne a yau alhamis su shiga yankin Musulmi Rakhin da ke kasar Myanmar domin ganin halin da musulmi suke ciki daga kusa.
-
ICC Ta Yi Watsi Da Bukatar Sake Laurent Gbagbo, Tsohon Shugaban Ivory Coast
Sep 27, 2017 13:03Kotun kasa da kasa mai shari'ar manyan laifuffukan yaki ta yi watsi da bukatar da a gabatar mata na ta saki Laurent Gbagbo, Tsohon Shugaban Ivory Coast da take tsare da shi.
-
Rawlings Ya Bukaci Trump Da Ya Kawo Karshen Kugen Yakin Da Yake Kadawa Kan Koriya Ta Arewa
Sep 27, 2017 13:03Tsohon shugaban kasar Ghana Jerry Rawlings ya kirayi shugaban kasar Amurka Donald Trump da ya kawo karshen barazanar da yake yi na kai hari kasar Koriya ta Arewa yana mai cewa wajibi ne yayi hakuri da yanayin siyasar shugaban Koriya ta Arewan kamar yadda duniya ta yi hakuri da yadda yake gudanar da mulkinsa shi ma.
-
Gwamnatin Venezuela Ta zargi Amurka Da Shishigi Cikin Lamurran Cikin Gida Na Kasar
Sep 27, 2017 09:06Ministan harkokin wajen kasar Venezuela Jorge Arasasa ya nuna rashin amincewarsa ga jawaban shugaban kasar Amurka da kuma Priministan kasar Espania a jiya Talata, ya kuma kara da cewa jawaban nasu shishigi ne a cikin lamurran cikin gida na kasar.