MDD Za Ta Binciki Zargin Aikata Laifukan Yaki A Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/world-i24487-mdd_za_ta_binciki_zargin_aikata_laifukan_yaki_a_yemen
Bayan shafe doguwar tattaunawa mai wuya, kwamitin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya, ya amunce da kudirin aikewa da wata tawagar kwararu na kasa da kasa don yin bincike kan zargin aikata laifukan yaki a kasar Yemen.
(last modified 2018-08-22T11:30:46+00:00 )
Sep 30, 2017 05:38 UTC
  • MDD Za Ta Binciki Zargin Aikata Laifukan Yaki A Yemen

Bayan shafe doguwar tattaunawa mai wuya, kwamitin kare hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya, ya amunce da kudirin aikewa da wata tawagar kwararu na kasa da kasa don yin bincike kan zargin aikata laifukan yaki a kasar Yemen.

Wannan dai na zuwa ne shekaru biyu da rabi bayan da kawacen soji da Saudiyya ke jagoranta ke kai hari kan 'yan gwagwarmayar neman sauyi na Houthis, da kawo yanzu ya janyi hasara rayukan mutane sama da 8,500 tare da raunana wasu 49,000.

Yakin da Saudiyya ke jagoranta ya kuma yi sanadin jefa kasar ta Yemen cikin wani bala'i da bai musultuwa, wanda hakan ya cilasta kwamitin kare hakkin bil adama na MDD aikewa da kwararu don binciken duk laifukan dake da nasaba da cin zarafin bil adama, da wuce gona da iri da ta'asar da duk bangarorin suka tafka tun daga watan Satumba na 2014.

Darektan bangaren bada shawarwari na kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa (FIDH), Antoine Madelin ya ce an sha wuya sosai kafin cimma wannan yarjejeniya, kasancewar Saudiyya na adawa da duk wani bincike a Yemen din, amman a cewarsa saboda nacewa da kuma goyan bayan da kasashen Canada da Netherlands suke da shi an samu amuncewar kafa kwamitin. 

Za'a dai nada kwararun da suka hada dana yankin dana kasa da kasa kafin karshen shekaran nan, kuma zasu bada rahoton a cikin shekara guda sannan za'a iya tsawaita aikinsu.