-
Sojojin Iraki Sun Kwato Sama Da 90% Na Garin Tal Afar Daga Hannun Da'esh
Aug 27, 2017 00:26Kakakin rundunar hadin gwiwa ta kasar Iraki Birgediya Janar Yahya Rasool ya bayyana cewar dakarun kasar da suke samun daukin dakarun sa kai na Hashd al-Sha'abi sun sami nasarar kwato sama da kashi 90% na birnin Tal Afar daga hannun 'yan ta'addan Da'esh, kuma nan gaba kadan za su kwace dukkanin birnin.
-
Yawan 'Yan Kasar Burundi Dake Gudun Hijra Zuwa Kasashen Makwabta Ya Karu
Aug 26, 2017 11:47Ci gaba da rikici gami da barazar da masu adawar gwamnati ke fuskanta a kasar Burundi ya tilastwa duban 'yan kasar hijra zuwa kasashen dake makwabtaka da kasar.
-
Shugaban Venezuela Ya Jaddada Wajibcin Kara Karfin Kariyar Kasar Don Fuskantar Barazanar Amurka
Aug 25, 2017 12:06Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bukaci kwamandojin sojin kasar da su kara himma wajen kara karfin kare kai da kasar take da shi don fuskantar barazanar wuce gona da irin Amurka.
-
MDD Ta Bukaci A Gudanar Da Bincike Kan Harin Da Saudiyya Ta Kai Yemen Shekaran Jiya
Aug 25, 2017 12:06Hukumar kula da hakkokin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci da a gudanar da wani bincike mai cin gashin kansa dangane da harin wuce gona da irin da Saudiyya da kawayenta suka kai kasar Yemen a shekaran jiya Laraba.
-
Sweden Za Ta Duba Yiwuwar Hana Shigo Da Naman Halal
Aug 25, 2017 00:47Majalisar dokokin kasar Sweden za ta gudanar da zama domin duba daftarin kudirin da ke neman a hana shigo da nama da aka yanka ta hanyar addini.
-
Jaridar Charlie Hebdo Ta Sake Buga Wani Zane Na Izgili Ga Muslunci
Aug 25, 2017 00:47Jaridar Charlie Hebdo da ake bugawa a kasar Faransa ta sake buga wani zane da ke yin izgili ga addinin musulunci, dangane da harin ta'addancin da aka kai a birnin Barcelona.
-
Shirin Jibge Dakarun Amurka A Afganistan, Bai Da Wani Tasiri_ Lavrov
Aug 24, 2017 11:58Sakataren harkokin wajen Rasha, Sergueï Lavrov, ya bayyana cewa shirin shugaba Donal Trump na jibge karin dakarun Amurka a Afganistan ba shi da wani tasiri.
-
Koriya Ta Arewa Ta Ce Babu Ja Da Baya Dangane Da Shirin Makamanta Masu Linzami
Aug 23, 2017 00:57Kasar Koriya ta Arewa ta bayyana cewar babu batun ja da baya ko cimma wata yarjejeniya dangane da shirinta na ci gaba da karfafa makamanta masu linzami ba.
-
Taliban Ta Mayar Da Martani Ga Shirin Trump Na Aikawa Da Karin Sojoji Afghanistan
Aug 23, 2017 00:56Kungiyar ta'addancin nan ta Taliban ta kasar Afghanistan ta yi barazanar cewa za ta mayar da kasar ta zama makabarta ga sojojin Amurka matukar dai gwamnatin ta aiwatar da shirinta na ci gaba da mamaye kasar Afghanistan din.
-
'Yan Buddha Sun Kaddamar Da Wasu Sabbin Shirye-Shiryen Takura Wa Musulmin Myammar
Aug 23, 2017 00:55Rahotanni daga kasar Myammar sun bayyana cewa mabiya addinin Buddha masu tsaurin ra'ayi sun kara killace wasu daruruwan musulmi Rohingya a jihar Rakhine a ci gaba da takura musu da suke yi.