Shirin Jibge Dakarun Amurka A Afganistan, Bai Da Wani Tasiri_ Lavrov
https://parstoday.ir/ha/news/world-i23504-shirin_jibge_dakarun_amurka_a_afganistan_bai_da_wani_tasiri_lavrov
Sakataren harkokin wajen Rasha, Sergueï Lavrov, ya bayyana cewa shirin shugaba Donal Trump na jibge karin dakarun Amurka a Afganistan ba shi da wani tasiri.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Aug 24, 2017 11:58 UTC
  • Shirin Jibge Dakarun Amurka A Afganistan, Bai Da Wani Tasiri_ Lavrov

Sakataren harkokin wajen Rasha, Sergueï Lavrov, ya bayyana cewa shirin shugaba Donal Trump na jibge karin dakarun Amurka a Afganistan ba shi da wani tasiri.

Mista Lavrov wanda ke bayyana hakan a wani taron manema labarai ya ce wannan shirin na Amurka ba shi da wani tasiri, hasali ma shirin ya karkata ne kan amfani da karfi.

Kasar ta Rasha ta bakin ministan harkokin wajen na ta, ta ce tana nadamar wannan sabon shiri na mahukuntan Washington.

A tsakiyar makon nan ne shugaba Trump ya bayyana shirin girke dakarun kasarsa a kasar ta  Afganistan, koda yake bai bayyana adaddinsu ba amma jami’an sa sun ce tuni ya amince da a tura karin sojoji 3,900 kan wadanda ke girke a kasar.

Fadar shugaban kasa a Afganistan dai ta yi maraba da matakin, inda Shugaban kasar  Ashraf Ghani ya bayyana cewa, '' hakan ya nuna cewa Amurka tana tare da su a ko da yaushe''