Sweden Za Ta Duba Yiwuwar Hana Shigo Da Naman Halal
(last modified Fri, 25 Aug 2017 05:17:49 GMT )
Aug 25, 2017 05:17 UTC
  • Sweden Za Ta Duba Yiwuwar Hana Shigo Da Naman Halal

Majalisar dokokin kasar Sweden za ta gudanar da zama domin duba daftarin kudirin da ke neman a hana shigo da nama da aka yanka ta hanyar addini.

Jaridar Daily Mail ta kasar Birtaniya ta bayar da rahoton cewa, majalisar dokokin kasar Sweden ta sanar da nan ba da jimawa ba za ta gudanar da zama na musamman, domin kada kuri’a kan daftarin kudirin da ke nemna a hana shigo da naman halal na musulmi da kuma yankan yahudawa a cikin kasar.

Tun kimanin watanni biyu da suka gabata ne wasu ‘yan majalisar dokokin kasar suka gabatar da wannan kudiri, wanda za a kada kuri’a a nasa, amma dai majalisar ba ta ayyana ranar gudanar da kada kuri’a a kan wannan daftarin kudiri ba.

Harburt Wniter shi ne shugaban babbar kungiyar yahudawa a kasar ta Sweden, ya bayyana cewa idan majalisar dokokin kasar ta amince da wannan daftari, to za a tauye musu wani bangare na hakkokinsu na addini.

Adadin mutane kasar Sweden dai ya kai kimanin miliyan 8, kimanin 17,500 yahudawa ne, yayin da adadin musulmin kasar ya kai dubu 450.