-
Antonio Guterres Ya Yi Suka Kan Barazanar Tsoma Bakin Kasashen Waje A Harkokin Kasar Venezuala
Aug 17, 2017 14:30Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana fatansa na ganin gwamnatin Venezuala da 'yan adawar kasar sun sulhunta tsakaninsu ta hanyar tattaunawa tare da yin kakkausar suka kan duk wata barazanar tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan kasar ta Venezuala.
-
An Halaka Wani Sojan Amurka A Afganistan
Aug 17, 2017 04:29Rundinar sojin Amurka a Afgnistan ta ce an kashe wani sajan ta a yakin da take da kungiyar 'yan ta'adda ta IS a yankin.
-
Donald Trump: Shugaban Koriya Ta Arewa Mutum Ne Mai Hikima
Aug 17, 2017 02:15Bayan kwashe tsawon watanni ana cacar baki da ma barazanar kai wa juna hari da manyan makamai a tsakanin gwamnatin Amurka da kuma Koriya ta arewa, shugaban kasar ta Amurka ya fito ya jinjina wa shugaban kasar Koriya ta arewa, tare da bayyana shi mutum mai hikima, sakamakon dakatar da harba makamai masu linzami da kasarsa ta shirya yi a kusa da tsibirin Guam.
-
Siriya Ta Zargi Amurka Da Kawayenta Da Taimakon 'Yan Ta'addan Kasar Da Muggan Makamai
Aug 17, 2017 01:07Kasar Siriya ta bayyana cewar Amurka, Birtaniyya da kawayensu suna goyon bayan 'yan ta'addan da suke yaki a kasar ta hanyar taimaka musu da sinadarori masu guba bugu da kari kan nau'oi daban-daban na makamai.
-
MDD Ta Bayyana Aniyarta Na Magance Rikicin Koriya Da Ya Kunno Kai
Aug 17, 2017 01:07Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewar rikicin da a halin yanzu ya kunno kai a tsibirin Koriya wani rikici ne maras tamka tsawon shekarun da suka gabata, don haka MDD a shirye take ta shigo don magance rikicin.
-
Wani Abu Ya Fashe A Tashar Filin Jiragen Sama Na Birnin Landan
Aug 16, 2017 14:51Rahotanni dake fitowa daga birnin Landan na kasar Birtaniya na cewa wani abu mai girma ya fashe a filin sauka da tashin na jiragen birnin Landan
-
M.D.Duniya Ta Yi Allah Wadai Da Harin Kunan Bakin Waken Da Aka Kai Jihar Bornon Nigeriya
Aug 16, 2017 07:17Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da hare-haren kunan bakin waken da aka kai garin Mandarari da ke jihar Borno a shiyar arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya a jiya Talata.
-
Ana Zargin Kungiyar Neo-Nazi Da Shirin Kai wa Musulmi Hari A Birtaniya
Aug 15, 2017 13:13Jami’an tsaron kasar Birtaniya sun fara farautar wasu mutane 40 Mambobi a kungiyar Neo-Nazi.
-
Babban Sakataren MDD Ya Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Kan Dakarun MDD A Mali
Aug 15, 2017 07:16Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi tofin Allah tsine tare da yin Allah wadai kan harin wuce gona da irin da aka kai kan dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Mali.
-
Pyongyang Ta Soke Shirin Harba Makami Mai Linzami Zuwa Amurka
Aug 15, 2017 01:54Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya ce ya dan tsaida shirinsa na harba makami mai linzami zuwa tsibirin Guam na Amurka dake yankin Pacifique.