Pyongyang Ta Soke Shirin Harba Makami Mai Linzami Zuwa Amurka
https://parstoday.ir/ha/news/world-i23192-pyongyang_ta_soke_shirin_harba_makami_mai_linzami_zuwa_amurka
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya ce ya dan tsaida shirinsa na harba makami mai linzami zuwa tsibirin Guam na Amurka dake yankin Pacifique.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Aug 15, 2017 06:24 UTC
  • Pyongyang Ta Soke Shirin Harba Makami Mai Linzami Zuwa Amurka

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya ce ya dan tsaida shirinsa na harba makami mai linzami zuwa tsibirin Guam na Amurka dake yankin Pacifique.

Saidai Mista Jong-Un ya ce  zai iya tada maganar da zarar Amurka ta sake yi ma kasarsa barazana.

Wannan dai a cewar masu sharhi na nuna yiwuwar samun mafita a riki na tsakanin kasashen Amurka da Koriya ta Arewa.

A makon da ya gabata ne Koriya ta Arewa ta yi barazana harba makamai masu linzami hudu da zasu bi ta kan Japon zuwa tsibirin  na Guam da ya kunshi wasu muhimman sansanin sojin Amurka.