Donald Trump: Shugaban Koriya Ta Arewa Mutum Ne Mai Hikima
(last modified Thu, 17 Aug 2017 06:45:21 GMT )
Aug 17, 2017 06:45 UTC
  • Donald Trump: Shugaban Koriya Ta Arewa Mutum Ne Mai Hikima

Bayan kwashe tsawon watanni ana cacar baki da ma barazanar kai wa juna hari da manyan makamai a tsakanin gwamnatin Amurka da kuma Koriya ta arewa, shugaban kasar ta Amurka ya fito ya jinjina wa shugaban kasar Koriya ta arewa, tare da bayyana shi mutum mai hikima, sakamakon dakatar da harba makamai masu linzami da kasarsa ta shirya yi a kusa da tsibirin Guam.

Wannan mataki da Trump ya dauka ya zo wa da dama daga cikin Amurkawa da mamaki, musamman ma ganin yadda yake ta babatu a kan Koriya ta arewa tamkar zai share kasar daga doron kasa, amma kuma a lokaci guda ya dawo yana yabon shugaban kasar wanda Trump ke bayyana shi a matsayin mutum mafi hadari ga Amurka, wanda hakan ya sanya wasu Amurkawa da suka hada har da 'yan majalisar dokokin kasar yin kakkausar suka a kan hakan, tare da bayyana cewa Trump ya zubar da kansa kasa warwas a gaban Koriya ta arewa.

A ranar Talata da ta gabata ce shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un ya bayyana cewa, zai dakatar da harba makamai masu linzami zuwa kusa da tsibirin Guam na Amurka, wanda Amurka ta kafa wani babban sansanin sojojinta a cikinsa, amma matukar Amurka ta ci gaba da yin barazana ga kasarsa, to kuwa babu abin da zai hana kasarsa harba wadannan makamai.

Amurka ta fara tunanin daukar matakin soji a kan Koriya ta arewa ne da sunan rusa makamanta na nukiliya tun a  cikin shekara ta 1994, kamar yadda tsohon mataimakin sakataren tsaron Amurka na lokacin Richard Perle ya bayyana, inda ya ce zai fi kyau su yi amfani da salon da Isra'ila ta yi amfani da shi wajen tarwatsa cibiyar nukiliya ta Saddam Hussain a kasar Iraki, ba tare da hakan ya cutar da sauran al'ummar Iraki ko mutane yankin gabas ta tsakiya ba.

Baya ga haka kuma, tsohon sakataren tsaron Amurka a lokacin shugabancin Bill Clinton William Perry, a wata zantawa da ta hada shi da jaridar Politico, wadda aka buga a ranar 15 ga watan Afirilun wannan shekara ta 2017, ya bayyana cewa a cikin shekara ta 1994 ya mika wa shugaban Amurka na lokacin Bill Clinton wani shiri da suka tsara, da nufin fuskantar barazanar hadarin makaman nukiliya daga kasar Koriya ta arewa, daga cikin shirin kuwa har da aikewa da dakarun Amurka 37,000 da za a girke su a yankin, musamman a cikin kasashe masu kawance da Amurka na yankin, da suka hada da Japan da kuma Koriya ta kudu.

A lokacin cacar baki ta tsananta  a tsakanin Koriya ta arewa da kuma gwamnatin Amurka a lokacin Bill Clinton, lamarin ya kusa ya kai bangarorin biyu ga gwabza yaki, amma daga bisani Bill Clinton ya sassauta kalamansa dangane da Koriya ta arewa, tare da janye barazanar kai mata harin soji, wanda daga karshe hakan ya bayar da dama har bangarorin biyu suka koma ga teburin tattaunawa.

Masana da dama suna bayyana abin da yake faruwa a halin yanzu tsakanin Amurka da Koriya ta arewa da cewa ya yi kama da abin da ya faru a lokacin shugabancin Bill Clinton, ma'ana kalaman barazanar kai wa Koriya ta arewa hari da Trump ke yi ba ta wuce barazana ta fatar baki ba, babban abin da ke kara tabbatar da hakan shi ne, yadda Trump ya yi gaggawar fitowa ya bayyana farin cikinsa da kuma nuna yabo ga shugaban Koriya ta arewa da bayyana shi a matsayin mutum mai hikima, kan dakatar da harba makamai a tsibirin Guam, tare da bayyana cewa kofar sulhu da tattaunawa tare da Koriya ta arewa a bude take, sabanin abin da aka saba ji daga bakin Trump da kuma jami'an gwamnatinsa.