-
EU Ta Baiwa Kasashen Sahel Yuro Miliyan 50 Don Yakar Ta'addanci
Jun 06, 2017 01:19Kungiyar tarayya turai ta sanar da baiwa kasashen yankin Sahel tallafin kudade da yawansu ya kai miliyan hamsin na Yuro, domin baiwa kasashen damar kafa wata rindinar hadin gwiwa domin yaki da ta'addanci.
-
Za'a Gudanar Da Zaben Majalisar Dokokin Venezueal A Karshen Wannan Watan
Jun 05, 2017 03:41Gwamnatin kasar Venezuela ta bada sanarwan cewa za'a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a ranar 30 ga watan yuli da muke ciki.
-
Majalisar Musulmin Birtaniya Ta Yi Allah wadai Da Harin London
Jun 05, 2017 02:08Majalisar musulmin kasar Birtaniya ta yi tir da Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a birnin London fadar mulkin kasar.
-
Koriya Ta Arewa Ta Yi Watsi Da Takunkumin Kwamitin Tsaron MDD
Jun 04, 2017 13:34Koriya ta Arewa ta yi watsi gaba daya da sabbin takunkumin da kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sanya wa wasu kamfanoni da jami'an kasar, tana me shan alwashin ci gaba da shirin nukiliya da makamanta masu linzami ba tare da bata lokaci ba.
-
Rahotanni: An Kai Gungun Hare-Haren Ta'addanci Birnin London
Jun 04, 2017 01:06Rahotanni daga birnin London na kasar Birtaniyya sun bayyana cewar an kai wasu jerin hare-hare a birnin na London a daren jiya da yayi sanadiyyar mutuwa da kuma raunana wasu mutane lamarin da 'yan sanda da kuma jami'an kasar suka bayyana da cewa wani hari ne na ta'addanci.
-
Kungiyar Kwallon Kafa Ta Real Madrid Ta Lashe Kofin Zakaran Zakarun Turai
Jun 04, 2017 01:05Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kasar Spain ta lashe gasar zakaran zakarun Turai bayan ta doke kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta kasar Italiya da ci 4-1 a wasan karshen da suka buga a birnin Cardiff da ke Birtaniya a daren jiya Asabar.
-
Marassa Karfi Na Samun Taimako Daga Musulmi A Birtaniya
Jun 03, 2017 15:51Mabiya addinin muslunci a birnin Northamptonchron na kasar Birtaniya suna taimaka ma sauran jama’a marassa karfi a cikin wannan wata.
-
Kungiyar ISIS Ta Bude Wani Masallaci A Asirce A Cikin Turkiya
Jun 03, 2017 15:47Kungiyar ‘yan ta’addan ISIS ta bude wani masallaci a asirce a gabashin birnin Istanbul na Turkiya domin hada ‘yan kungiyar wuri guda a Turkiya.
-
Hukumar Leken Asirin Amurka Ta CIA Ta Bude Wani Bangare Na Musamman Kan Kasar Iran
Jun 03, 2017 02:28Hukumar leken asirin Amurka ta CIA ta bude wani bangare na musamman da zai din ga gudanar da ayyukan leken asiri kan kasar Iran.
-
Rasha Ta Ce Takunkumin Da Wasu Kasashen Yammacin Turai Suka Kakaba Mata Baya Kan Doka
Jun 03, 2017 02:27Shugabar Majalisar Dokokin kasar Rasha ta bayyana cewa: Takunkumin da wasu kasashen yammacin Turai suka kakaba kan kasarta ta Rasha ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa.