Majalisar Musulmin Birtaniya Ta Yi Allah wadai Da Harin London
(last modified Mon, 05 Jun 2017 06:38:39 GMT )
Jun 05, 2017 06:38 UTC
  • Majalisar Musulmin Birtaniya Ta Yi Allah wadai Da Harin London

Majalisar musulmin kasar Birtaniya ta yi tir da Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai a birnin London fadar mulkin kasar.

tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da majalisar musulmin kasar Birtaniya ta fitar a jiya, ta yi Allah wadai da kakakusar murya da wannan aiki wanda ta bayyana shi da cewa na ta’addanci ne.

Bayanin ya ci gaba da cewa, musulmin kasar Birtaniya suna taya dukkanin iyalan wadanda abin ya rutsa da su alhin abin da ya faru, tare da bayyana wadanda suka kai harin da cewa mutane masu kesassar zuciya, kuma abin da suka yi ba shi da wata dangantaka da wani addini, domin kuwa a cewar bayanin aikata ta’addanci da kisan bil adama da cusa tsoro a cikin zukatan jama’a da sunan addinin musulunci, hakan yana a matsayin tozarci ne ga addinin muslunci.

A cikin daren Asabar da ta gabata ce aka kai harin na birnin London, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 da kuma maharani su uku.

Kungiyar 'yan ta'addan wahabiyyah takfiriyyah ta ISIS dai ta dauki alhakin kai harin.