Rasha Da Burtaniya Sun Dawo Da Huldar Tattaunawa Tsakaninsu
Mahukuntan Moscow da Landon sun dawo da huldar diflomatsiya tattaunawa a tsakaninsu bayan shafe watanni 11, tun bayan kiki-kakar da ya shiga tsakaninsu kan batun jami'an leken asirin nan na Rasha Skripal.
Hakan dai ya biyo bayan ganawar da sakataren kula da harkokin Biritaniya na Turai, Alan Duncan, da kuma mukadashin ministan harkokin wajen Rasha, Vladimir Titov, sukayi a daura da taron kasa da kasa na Munich, kan tsaro.
Wannan dai ita ce ganawa ta wasu manyan jami'an gwamnatocin kasashen biyu cikin watanni 11.
Sanarwar da Biritaniya ta fitar, ta ce har yanzu akwa sabani a bangarori da dama tsakaninsu da Rasha, tare da bukatarta Rasha data canza halayenta, musamman kan damuwar da kasashen duniya keda kan ayyukanta a Ukraine da kuma kan al'ummar Tchétchénie.
Saidai wata sanarwa da Rasha ta fitar, ta ce sanarwar da Londan ta fitar babu kamshin gaskia ko guda a ciki, kuma sam sunyi hannu riga da batutuwan da bangarorin suka tattauna kansu, hasali a cewarta bangaren na Biritaniya ne ya bukaci tattaunawar.
Tattaunawa tsakanin kasashen biyu ta katse ne tun a ranar 14 ga watan Maris na 2018, bayan da firaministar ta Burtaniya, Theresa May, ta sanar da dakatar da duk wata tattaunawa ta tsakanin manyan jami'an kasashen, a matsayin maida martani kan zargin Rasha da hannu a harin sinadario mai guda da aka kan jami'in Skripal.